Hukumar shirya jarabawar share fagen shiga Jami’o’i ta Nijeriya JAMB, ta fitar da mafi kankantar makin da ake bukata domin samun damar shiga manyan makarantu a zangon karatu na shekara ta 2022 da 2023.
Shugaban hukumar Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana haka, bayan ganawa da shugabannin jami’o’i, da na kwalejojin fasaha da na ilimi na Nijeriya, inda ya ce kowace makaranta ta na da damar sanya makin da ta ke bukata har zuwa maki 220.
Farfesa Ishaq Oloyede ya kara da cewa, babu makarantar da za ta dauki dalibi da kasa da makin da aka amince da shi.
An dai amince wa kwalejojin fasaha da na ilimi maki 100, yayin da aka amince da mafi kankantar maki 140 ga jami’o’in Nijeriya.

