Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ilimi: Hukumar JAMB Za Ta Saki Sakamakon Jarrabawa

Hukumar shirya jarrawabar sharar fage ta shiga jami’o’i wato JAMB, ta ce a nan ba da jimawa ba za ta aika da sakonni ta wayar salula ga dalibai domin sanar da su akan lokacin da za ta saki sakamakon jarrabawar bana.

Hukumar ta ce kwanannan za ta tura sakonni ga dalibai masu neman shiga jami’o’i domin sanar da su akan lokacin da za ta saki sakamakon jarrabawar bana da zarar ta kammala tantancewa.

Jami’in yada labarai na hukumar Dakta Fabian Benjamin, ya bayyanar haka a  cikin wata hira da ya yi da manema labarai a Legas.

Benjamin ya nemi dalibai da su kauracewa sauraron masu yada labarun kanzon kurege akan sakamakon jarrabawar bana musamman a kafofin sada zumunta.

Rahotanni sun bayyana cewa, fiye da dalibai miliyan 1 da dubu dari 8 masu neman shiga jami’o’i ne suka yi jarrabawar JAMB a jihohi da ke Najeriya.

Hukumar JAMB ta yaba da salo da tsari da kuma yanayi na gudanar da jarrabawar bana, musamman yadda aka tsarkake magudin  jarrabawa.

Exit mobile version