Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

JAMB Ta Haramta Wa Dalibar Da Ta Yi Sakamakon Bogi Sake Zana Jarabawa

Hukumar Shirya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a JAMB, ta haramta ma wata daliba mai suna Mmesoma Ejikeme da ake zargi da fitar da sakamakon jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire zana jarrabawa har tsawon shekaru uku.

Wannan dai ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban hukumar JAMB Dakta Fabian Benjamin ya fitar.

Hukumar, wadda ta gano sakamakon jarabawar da Mmesoma ta buga na bogi ne, ta nanata cewa tuni ta dakatar da sakamakon dalibar.

Haka kuma, hukumar ta ba ‘yan Nijeriya tabbacin cewa ba a yi mata kutse a cikin manhajar ta ta adana sakamakon jarrabawar ba, musamman ganin yadda wasu daliban su ka yi kwafin sakamakon jarrabawar na bogi da wata mai suna Asimiyu Mariam Omobolanle, wadda ta zauna zana jararrabawar ta a shekara ta 2021 har ta samu makin da ya kai 138.

Ta ce za su cigaba da kare mutuncin su, ta na mai nanata bayanin ta na baya cewa sakamakon da dalibar ta gabatar cewa ta samu maki 138 a jarabawar shekara ta 2021 na bogi ne.

Exit mobile version