Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

NECO Ta Fitar Da Sakamakon Jarabawar 2019

Hukumar shirya jarrabawar kammala karatun sakandare ta NECO, ta saki sakamakon jarrabawar watan Yuni da Yuli na shekara ta 2019.

Bisa ga sakamakon da hukumar ta saki, dalibai dubu 829 da 787 sun samu nasara a kan darussa biyar ciki har da harshen turanci da kuma darasin lissafi.

Hakan kuwa ya na nufin an samu karuwar kasa  da kashi daya cikin 100 idan aka kwatanta da sakamakon jarrabawar shekara ta 2018.

Idan dai za a iya tunawa, a baya rahotanni sun ce mai yiwuwa hukumar shirya jarrabawar JAMB ta soke fiye da rabin sakamon jarrabawar da aka yi a shekara ta 2019 a wasu jihohin kasar nan, kamar yadda wani ma’aikacin hukumar ya shaida wa manema labarai.

Jami’in, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce hukumar JAMB za ta soke sakamakon jarrabawar ne saboda magudin da aka tafka yayin rubuta jarrabawar da aka yi tsakanin ranakun 11 zuwa 18 ga watan Afrilu.

Exit mobile version