Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Hukumar Shige-Da-Fice Ta Dakatar Da Jami’in Ta

OIF

OIF

Hukumar (NIS) ta dakatar da Mataimakin Sufeton Shige da Fice bisa zargin karɓar kudi daga wani matafiyi.

Shugaban Hukumar, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, ya fitar a Abuja.

A cewar Nandap, halayen jami’in, wanda aka ɗauka a wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta,

bai nuna shi jami’i ne mai nagarta ba.

Sanarwa ta kuma ta ce hukumar ta yi Allah wadai da kakkausar harshe kan rashin da’ar da jami’in ya nuna,

tana mai cewa hakan ya kawo cikas ga sauye-sauyen da ake yi da nufin inganta ayyukan hukumar.

Ta ba da tabbacin cewa an dakatar da jami’in ne har sai an kammala bincike bisa tsarin ladabtarwa,

kamar yadda doka da kuma dokokin aikin gwamnati suka tanada.

hukumar ta samu faifan bidiyon ne da ke yawo a kafafen sada zumunta mai taken “Yadda jami’an shige-da-fice ke musgunawa masu yawon bude ido a Najeriya,”

wanda ke nuna yadda daya daga cikin jami’anta ke neman kudi daga wani matafiyi.

Exit mobile version