Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Harin Jirgi: Tinubu Ya Ba Gwamnatin Kaduna Gudunmawar Naira Miliyan 50

Jagoran jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya ba gwamnatin
jihar Kaduna gudunmawar naira miliyan 50 domin ɗawainiyar
waɗanda harin jirgin kasa ya rutsa da su.

Bola Tinubu ya bayyana kyautar ne yayin da ya ke jawabi a
fadar gwamnatin jihar Kaduna, lokacin da kai gwamna El-Rufa’i
ziyarar jaje bisa abin da ya faru.

Ya ce kuɗin ya bada su ne a matsayin gudunmawa ga
gwamnatin jihar Kaduna, domin kula da waɗanda su ka jikkita a
harin da kuma tallafi ga gwamnatin jihar ta ɗawainiyar da ta ke
yi.

Idan dai ba a manta ba, ‘yan bindiga sun kai hari a kan jirgin
kasa daga Abuja zuwa Kaduna.

Exit mobile version