Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Gwamnatin Tarayya Ta Bankado Ma’aikata 1,618 Masu Takardun Daukar Aikin Bogi

Gwamnatin tarayya ta ce ta bankado ma’aikatan da aka dauka
aiki da takardun bogi guda dubu 1 da 618.

Shugaban ma’aikatan tarayya Folashade Yemi-Esan ta bayyana haka, a wani taron manema labarai kafin gudanar da makon ma’aikata na shekara ta 2023.

Folashade, ta ce gwamnatin tarayya ta bankado ma’aikatan ne a cikin tsarin biyan albashi na IPPIS.

Ta ce an kuma gano wasu ma’aikata dubu 69 da 854 a wasu manyan ma’aikatun gwamnatin tarayya da hukumomin gwamnatin tarayya da ke shiyyoyi shida na Nijeriya da birinin tarayya Abuja.

Folashade Yemi-Esan ta kara da cewa, bisa aikin da ake ci- gaba da gudanarwa, an dakatar da wasu ma’aikatan daga cikin tsarin albashi na IPPIS.

Exit mobile version