Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Karin Albashi: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Biyan Kananan Ma’aikata Naira 30,000 – Ngige

Tsarin IPPIS: Yajin Aiki Kungiyar ASUU Haramtaccene - Ngige

Tsarin IPPIS: Yajin Aiki Kungiyar ASUU Haramtaccene - Ngige

Ministan kwadago Chris Ngige, ya ce gwamnatin tarayya ta fara biyan Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikatan da aka dade ana fsa-in-sa a kai.

Chris Ngige, ya ce gwamnatin tarayya ta fara biyan ma’aikatan sabon karin albashin ne, domin ta dauki karin da muhimmanci kamar yadda kungiyoyin kwadago su ka bukata.

Ministan ya bayyana haka ne, yayin wata zantawa da ya yi da manema labarai, inda ya ce naira dubu 30 na karamin ma’aikaci matakin karshe ne a wajen aiki.

Ya ce sun samu matsala ne a kan karin da za a yi wa wadanda ke mataki na 7 zuwa 14, wadanda su ne Ma’ikatan da su ke karbar abin da ya haura sabon mafi karancin albashin. Ministan ya yi ikirarin cewa, ana samun matsala wajen dabbaka sabon albashin ne, wajen tattaunawar da ake ci-gaba da yi tsakanin gwamnati da bangaren ‘yan kwadago, amma ya ce ya na sa ran za a kara albashin ta yadda zai shafi kowane matakin aikin gwamnati.

Exit mobile version