Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Gwamnatin kano ta yi binciken kwakwaf kan faifen ganduje na dala

Gwamnatin jihar Kano ta karbi rahoton kwararru masu
binciken kwakwaf game da faifen bidiyon Dala da ya nuna
tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya na
sunkumawa a aljihun sa, inda ake zargin cewa ya karba ne a
matsayin cin hanci daga ‘yan kwangila.

Har yanzu dai gwamnatin jihar Kano ba ta yi wa jama’a bayani game da sakamakon binciken da ta tattara ba, inda ta ce ta na kan nazartar sakamakon.

Gabanin zaben shekara ta 2019 ne, wani faifen bidiyo da editan Jaridan Daily Najeriya Jafar Jafar ya wallafa, ya nuna yadda Ganduje ya ke karbar daloli daga wani da ba a bayyana fuskar sa a faifen ba.

Tuni dai gwamnatin jihar Kano ta bude bincike da nufin tabbatar da ganin an yi hukunci a kan zarge-zargen karbar cin hancin da aka ce tsohon gwamnan ya yi.

Exit mobile version