Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kotu Ta Bayar Da Umarnin Sakin Tsohon Kwamishinan Ganduje

Babbar kotun tarayya da ke Kano, ta bada umarnin a saki
tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Injiniya Idris Wada
Saleh da ake zargi da almundahanar naira biliyan ɗaya.

A baya-bayan nan ne, babbar kotun Majistare ta jihar ta umarci a tsare shi a hannun hukumar karɓar ƙorafe- ƙorafe da hana cin hanci ta jihar Kano, bisa zargin yaudara da yin karya a takardun wasu ayyuka zamanin gwamnatin Ganduje.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano dai ta yi zargin cewa, a shekara ta 2023, tsohon kwamishinan ya ba kamfanin Arafat da ‘Multi resources’ nairan biliyan ɗaya domin gyaran tituna 30 a cikin birnin Kano, sai daihukumar ta ce babu ko ɗaya daga cikin ayyukan da aka yi.

Idan dai baa manta ba, hukumar ta ce ta aike da takardar gayyata ga tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje a kan ‘bidiyon dala, amma babbar kotun tarayya da ke jihar ta dakatar da hukumar a kan wannan lamari, har sai zuwa lokacin da za ta kammala sauraren ƙorafin da Ganduje ya shigar ya na neman ta hana hukumar binciken sa.

Exit mobile version