Gwamnatin jihar Kogi, ta dakatar da mai martaba Sarkin Eganyi Alhaji Musa Isa Achuja daga mukamin sa sakamakon tabarbarewar tsaro a yankin sa.
Gwamna Yahaya Bello ya bada umurnin dakatar da basaraken ne, bisa zargin sa da yin saku-saku da al’amurran da su ka shafi tsaro a yankin karamar hukumar Ajaokuta, bayan wani bincike da jami’an tsaro su ka yi, lamarin da ya sa a karshe su ka kama sarkin.
Gwamnan, ya kuma bada umurnin a rubuta wasikar tuhuma ga shugaban karamar hukumar Ajaokuta Mustapha Aka’aba, domin ya wanke kan shi dangane da yadda tsaro ya tabarbare a yankin.
A ranar Asabar din ta da gabata ne, ‘yan bindiga su ka yi ma wasu ‘yan sanda uku ciki har da DPO da wasu ‘yan sa-kai su biyar kwanton-bauna a yankin karamar hukumar, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen takwas baki daya.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Mohammed Onogwu ya sanya wa hannu, gwamna Yahaya Bello ya gargadi sarakunan jihar Kogi su guji hada-baki ko taimaka wa miyagu ta kowace hanya wajen yin aika-aika a jihar, ya na mai cewa gwamnatin shi za ta sa kafar-wando guda da duk mutumin da ke goya wa ‘yan ta`adda baya komai girman sa.