Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Rashin Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Tilasta Wa Jama’ar Shinkafi Kwana A Daji

'Yan Bindiga

'Yan Bindiga

‘Yan bindiga, sun tilasta wa jama’ar Karamar Hukumar Shinkafi da ke jihar Zamfara kwana a cikin daji, sakamakon farmakin da su ka kai masu, inda suka yi awon gaba da akalla mutane 40 da su ka hada da wasu ‘yan kasar Ghana.
Jama’ar yankin sun shaida wa manema labarai cewa, sun yi ta kabbara da kiran sallah da nufin samun kwarin gwiwar tunkarar ‘yan bindigar.

Sarkin Shanun Shinkafi Dakta Sulaiman Shu’aibu, ya bayyana takaicin sa da yadda sojoji su ka ki kai masu dauki har sai da ‘yan bindigar su ka ci galabar su.

Ya ce daga yanzu babu wani sauran kwarin gwiwa da su ke da shi a kan sojojin Nijeriya, domin sun gaza gudanar da ayyukan su na kare rayukan al’ummar yankin.

Dakta Shinkafi ya kara da cewa, daga yanzu za su cigaba da dogaro da kawunan su wajen samar da kariya daga ‘yan bindigar saboda jami’an tsaron sun kasa.

Exit mobile version