Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya ƙwace fitaccen asibitin yara na Hasiya Bayero da ke cikin birnin Kano.
Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne, a wata ziyara da ya kai asibitin domin duba halin da asibitin ke ciki.
Asibitin dai ya shafe tsawon shekaru 33 ya na aiki, wanda ya shahara wajen karɓar yara marasa lafiya daga ilahirin ƙananan hukumomin jihar Kano da kuma maƙwaftan jihohi.
Gwamna Abba ya bada umarnin a gyara asibitin nan take zuwa na zamani domin al’umma su cigaba da cin moriyar sa.
Haka kuma, Gwamnan ya nuna ɓacin ran sa da yadda ana tsaka da amfani da asibitin, amma gwamnatin Ganduje ta saida shi ta kuma tada jama’a marasa lafiya da likitoci.
Gmamnan ya jaddada cewa, duk wanda aka ba asibitin Hasiya Bayero sun ƙwace shi sun maida wa talakawa haƙƙin su, bayan gwamnatin Ganduje ta saida asibitin a kan Naira miliyan 6.

