Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Gargaɗin INEC: Ba Za Mu Ƙara Wa’adin Zaɓen Fidda Gwanaye Ba

Hukumar Zaɓe mai zaman kan ta ta Ƙasa inec, ta nanata matsayin ta cewa ba za ta ƙara wa’adin da ta tsara na gudanar da zaɓuɓɓukan fidda gwani na jam’iyyun siyasa ba.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka, a wajen wani taro da a kan yi da jam’iyyun siyasa duk bayan wanni hu]u a Abuja.

Farfesa Mahmud, ya ce akwai ayyuka da dama da masu alaƙa da juna a kan batun wa’adin zaɓuɓɓukan, waɗanda dole ne a aiwatar da su.

Ya ce duk wani sauyi da za a yi ma wa’adin zai iya shafar sauran ayyukan ta yadda ba a so, kuma yin hakan zai kawo matsaloli ga jam’iyyun da ita kan ta hukumar zabe.

Farfesa Yakubu, ya ce lokacin da jam’iyyun su ka ware domin yin zaɓuɓɓukan fidda gwani ya fara ne daga ranar 4 ga watan Afrilu na shekara ta 2022, kuma zai ƙare a ranar 3 ga yuni na shekara ta 2022.

Exit mobile version