Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Aikin Zabe: Jihohin Kogi Da Bayelsa Na Da Wuyar Sha’ani – INEC

Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta kasa, INEC

Shugaban Hukumar Zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce idan ana batun sha’anin gudanar da zabe, to jihohin Kogi da Bayelsa su na da wahalar sha’ani.

Farfesa Yakubu ya bayyana haka ne, yayin wani taron neman goyon bayan sarakunan gargajiya na Jihar Bayelsa, don tabbatar da ganin an gudanar da zaben gwamnan jihar lami lafiya.

Ya ce halayyar da manyan ‘yan siyasar jihohin biyu ke nunawa a lokutan zabe, abu ne mai kawo wa hukumar  Kalubale ba karami ba.

Yakubu ya kara da cewa, an ga yadda aka yi kakudubar gudanar da zabubbukan fidda-gwani a jihohin biyu, an kuma fara yakin neman zabe, kuma za a ci-gaba da yi har zuwa ana saura sa’o’i 24 a fara zabe.

A karshe Farfesan ya ce, ya ce za a yi amfani da ma’aikatan zabe 10,000 a Jihar Bayelsa, yayin da a tura ma’aikata 14,000  jihar Kogi.

Exit mobile version