Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Dokar Hana Fita: Jihar Legas Ta Shirya

Dokar Hana Fita: Jihar Legas Ta Shirya.

Dokar Hana Fita: Jihar Legas Ta Shirya.

Gwamnatin jihar Legas ta ce a shirye take ta aiwatar da dokar hana fita na kwana 14 a fadin jihar.

Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu ya sanar da hakan, yan sa’o’i bayan shugaba Kasa Muhammadu Buhari ya ayyana dokar da za ta fara aiki da karfe 11 na daren Litinin 30 ga Maris, 2020.

“Ina tabbatar muku cewa za mu yi dukkan abin da za mu iya domin ganin jama’a ba su tagayyara ba saboda dokar,” a cewar Sanwo-Olu.

Shugaba Buhari ya ayyana dokar ne domin hana yaduwar annobar coronavirus, wadda ta fi kamari a jihar Legas.

Sanwo-Olu ya bayyana shirin gwamnatin jihar Legas ne a sakonsa na ba wa ‘yan ‘yan jihar kwarin gwiwa kan fargabar da suke nunawa  na matsatsin rayuwa da dokar za ta haifar.

Ya ce tuni gwamnatin jihar ta yi shiri domin irin wannan yanayi.

Gwamnan ya kara da cewa za a yi amfani da lokacin dokar ne wurin takaita yaduwar cutar coronavirus.

“Dokar ta shafi dukkan mazauna jihar Legas. 

“Wadanda ba ta shafa ba su ne cibiyoyin da kamfanonin kiwon lafiya; masana’antu sarrafa abinci da gidajen abinci; kamfanonin lantarki; kamfanoni da masu dakon mai; da kuma kamfanonin tsaro.

“Za yi amfani da lokacin wurin ganowa, bibiya da killace wadanda suka kamu da cutar.

“Za kuma mu tabbatar an yi wa masu cutar magani tare da hana ta yaduwa zuwa wasu jihohi.

“Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Legas na aiki tare da Cibiyar Hana Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) domin ganin masu cutar sun samu ingantacciyar kulawa.

“Ku sani cewa za mu yi dukkan mai yiwuwa don ganin jama’a ba su tagayyara ta dalilin wannan doka ba.”

Dokar ta kuma shafi garuruwa masu makwabtaka da jihar Legas. Ta kuma shafi da kuma makwabciyarta, wato jihar Ogun.

 Kazalika Gwamnatin Tarayya ta sanya dokar hana fita a Babban Birnin Tarayya Abuja, wanda shi ne ke biye da jihar Legas wurin yawan masu cutar.

Exit mobile version