Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tsawaita Doka: Gwamnati Za Ta Cigaba Da Rabon Tallafin Abinci Ga Talakawa – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnati za ta cigaba da rabon kudi da kayayyakin abinci ga talakawa a dai-dai lokacin da aka kara wa’adin dokar hana shiga da fita a jihohi Legas da Ogun da kuma Abuja.

Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke gabatar da jawabi ga ‘yan Nijeriya a daren Litinin din da ta gabata, inda ya ce ya tsawaita dokar zuwa makonni 2 ne sakamakon shawarwarin da ya samu daga kwararru.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, tsawaita dokar ya zama dole domin kare yaduwar cutar Coronavirus a Nijeriya, musamman duba da cewa an fi samu yawan masu dauke da cutar jihar Legas da kuma Abuja.

Kididdiga daga cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC ta nuna cewa, akwai fiye da mutane 300 da ke dauke da cutar a Nijeriya, wanda yawancin su sun fito ne daga jihar Legas da Abuja.

Shugaba Buhari ya ce bisa tsawaita dokar, ita ma gwamnatin tarayya za ta tsawaita rabon kudi mda kayayyakin tallafin abincin ga talakawa, domin rage musu radadin halin da ake ciki.

Exit mobile version