Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kauran Bauchi Ya Ce Zai Buga Da Duk Wanda Ya Fito Takarar Shugaban Kasa

Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Muhamamd, ya ce a shirye ya ke ya ƙalubalanci duk wanda ya fito takara a zaɓen shugaban kasa na shekara ta 2023.

Yain da ya ke bayyana wa manema labarai kudirin shi na tsayawa takara, Bala Mohammed ya ce ba ya shaƙƙun kowa kuma zai fafata da duk wanda ya fito neman kujerar shugaban kasa.

Sanatan, ya ce muddin jam’iyyar PDP ta na son yin adalci, ya kamata ta tsaida ɗan takarar ta daga yankin arewacin Nijeriya.

Kalaman gwamnan dais u na zuwa ne, bayan wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonthan game da batun takarar sa, inda ya ce gwamnonin jihohin kudancin Nijeriya na jam’iyyar PDP ba su da hujjar cewa sai jam’iyyar ta fitar da dantakarar ta daga kudu.

Exit mobile version