Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Daruruwa Sun Yi Zanga-Zangar Adawa Da Gwamnatin Sojin Chadi

Daruruwan mutane sun fita zanga-zangar adawa da gwamnatin mulkin sojin Chadi a birnin N’Djamena, yayin da ake ci-gaba da zaman tankiya a kasar, biyo bayan mutuwar Idriss Deby.


An samu tashin hankali a kasar a watan Agustan nan, bayan kungiyoyin fararen hula sun yi kira da a fito gangamin nuna kyama ga gwamnatin sojin kasar, a karkashin dan marigayi Idriss Deby, Mahamat Idriss Deby Itno.


Masu zanga zangar sun caccaki Faransa, wadda ta yi wa kasar mulkin mallaka, su na mai zargin ta da goya wa sojoji baya su mulki kasar.
Idriss Debby dai ya mutu ne ya na da shekaru 68, bayan ya shafe fiye da shekaru 30 ya na mulkin kasar.

Exit mobile version