Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Chadi Ta Yi Wa Daruruwan ‘Yan Tawaye Afuwa

Gwamnatin sojin Chadi ta yi wa ƴan tawayen ƙasar kusan 300 afuwa da wasu ƴan siyasa, domin cika ɗaya daga cikin buƙatun ƴan adawa da aka gayyata taro kan makomar ƙasar.

Waɗanda aka yi wa afuwar 296 an ɗaure su ne kan laifuka da suka zafi na ta’addanci da kuma laifukan da suka shafi saɓawa ƙasa, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na AFP ya ruwaito.

Ƴan tawayen sun ce yin afuwar zai share fagen tayin tattauna da shugaba Mahamat Idriss Deby ya yi wanda ya karɓi shugabancin Chadi bayan mutuwar mahaifin sa da aka kashe a fagen daga a watan Afrilu.

Mahamat mai shekara 37 ya rusa gwamnati da majalisa tare da sauya kundin tsarin mulki inda ya yi alƙawalin gudanar da zaɓe cikin wata 18.

Baya ga yin afuwa, buƙatun ƴan tawayen sun ƙunshi yin afuwa ga dukkanin shugabannin siyasa da na soja da kuma dawo da ƙadarorin da gwamnati ta ƙwace.

Exit mobile version