Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Dan Bindiga Dake Jinyar Rauni A Asibiti Ya Shiga Hannu

NIGERIAN POLICE WITH RIFLE TheCable0 e1638223533511 1280x720 copy

NIGERIAN POLICE WITH RIFLE TheCable0 e1638223533511 1280x720 copy

Rundunar ’yan sandan jihar Filato ta kama wani ɗan bindiga a lokacin da yake jinyar raunin harbin bindiga a wani asibiti.

Maimagna da yawun rundunar, Alabo Alfred, ya ce ɗaya daga cikin ’yan bindigar da aka kama yana cikin waɗanda suka kai hari a unguwar Zurack da ke ƙaramar hukumar Wase ta jihar.

Alfred ya ce ’yan sandan sun kashe ’yan bindiga bakwai a wani mummunan farmaki da haɗin gwiwar rundunar DSS da wasu jami’an tsaro suka kai a dajin Bangalala na ƙaramar hukumar Wase.

Ya ƙara da cewa an miƙa ’yan bindigar da aka kama zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar domin gudanar da bincike mai zurfi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, an kashe ’yan bindiga bakwai a farmakin haɗin gwiwar na dajin Bangalala na ƙaramar hukumar Wase ta Jihar Filato, mai iyaka da jihohin Filato.

Ya ce sauran ’yan bindigan da suka gudu a yayin farmakin sun kai hari a ƙauyukan Zurak da Dakai, suka kashe mutane tara tare da ƙona gidaje shida.

Bayan faruwar lamarin, kwamishinan ’yan sandan jihar Filato ya ƙara tura jami’an sa yankin inda ya umarci kwamandan yankin ya mayar da sansanin sa zuwa ƙaramar hukumar Wase nan take.

Exit mobile version