Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Sojoji Sun Fatattaki ’Yan Bindiga A Filato

Rundunar Sojin Nijeriya, ta ce dakarun da aka tura garin
Mangu na Jihar Filato domin magance rikicin da ke faruwa
sun kashe wasu ‘yan bindiga da dama.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya wallafa a shafin rundunar na yanar gizo, ta ce lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Mangu mai fama da rikicin ƙabilanci ranar Larabar da ta gabata.

Wannan dai ya na zuwa ne, kwanaki kaɗan bayan hukumomin jihar sun sa dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Mangu, bayan ɓarkewar rikicin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Birgediya Janar Nwachukwu. Ya ce dakarun rundunar da aka tura domin shawo kan rikicin da ke faruwa a Ƙaramar Hukumar Mangu sun kashe ‘yan bindiga da dama lokacin da ‘yan bindigar su ka yi musu kwanton-ɓauna.

Rundunar ta ce ta share dajin da ’yan bindigar su ke samun mafaka, inda ta gano bindigogi uku ƙirar AK 47, da harsasai 14 na musamman, da babur ɗaya da kuma katin shaida na wani ƙaramin ɗan sanda.

Exit mobile version