Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Daliban Najeriya 700 Sun Samu Guraben Karatu A Amurka

Ofisoshin Jakadancin Amurka da ke Abuja da Lagos, sun gudanar da taron wayar da kan daruruwan daliban Nijeriya da su ka samu guraben karatu a jami’o’i da kwalejojin Amurka

Kimanin daliban Nijeriya dari bakwai ne su ka samu guraben karo karatu a Amurka, a karkashin wani shirin bada tallafin karatu na gwamnatin Amurka mai suna ‘Education USA, wadanda ake sa ran nan gaba kadan za su tashi.

Shirin dai na ma’aikatar harkokikn wajen Amurka ne da ke mara wa cibiyoyi dari 430 na daliban kasashen duniya, domin samun guraben karatu da bada tallafin karatu ga ‘ya’yan talakawa.

A shekarar da ta gabata, kimanin daliban Nijeriya dubu 14 ne su ka samu guraben karatu a jami’o’i da makarantu daban-daban a Amurka, inda Nijeriya ta kasance kasa ta goma a duk duniya da daliban ta su ka fi samun guraben karatu.

Jami’an diflomasiyyar Amurka, sun yi fatan daliban Nijeriya da ake sa ran su zama manyan gobe, za su taimaka wajen bunkasa da kuma ci-gaban kasar su a gaba.

Exit mobile version