Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Dokar Bayar Da Bashin Karatu Za Ta Kori ’Ya’yan Talakawa Da Yawa Daga Makarantu – ASUU

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa ASUU ta yi gargadin cewa, idan ba a yi hankali ba kwanan nan dokar bada rance ga dalibai za ta kori ‘ya’yan talakawa daga makarantu.

A ranar Litinin da ta gabata ne, Shugaba Tinubu ya sa hannu a kan dokar da za ta ba daliban manyan makarantu masu karamin karfi damar cin bashin karatu daga gwamnati su biya daga baya.

Mutane da dama dai sun yi ta jinjina wa Tinubu, inda su ka ce ya cika alkawarin da ya dauka lokacin yakin neman zabe, sai dai Shugaban kungiyar ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce dokar za ta iya kawo cikas ga dalibai masu karamin karfi da dama.

Ya ce babbar fargabar su ita ce dokar za ta iya sa makarantu su kara samun kudaden karatu, wanda hakan zai shafi miliyoyin daliban da ke karatu a manyan makarantun Nijeriya.

Farfesa Emmanuel ya ce dokar ba sabuwa ba ce, domin ko a lokacin mulkin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari sai da su ka yake ta, sai dai ya ce har yanzu kungiyar ba ta samu nazartar dukkan kundin sabuwar dokar da Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu ba.

Exit mobile version