Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Dalibai Sun Rufe Hanyoyin Ife-Ibadan Da Lagos-Abeokuta

Wasu taliban jami’a sun yi zanga-zanga don ganin an kawo karshen yajin aikin kungiyar ASUU, sannan su ka ce za su cigaba da yin bore har sai malaman jami’o’i sun janye yajin aikin da su ke yi tare da sake bude makarantu don ci-gaba da karatu.

Taruruwan taliban ne su ka rufe manyan hanyoyin da su ka tashi daga Ibadan da Elesa da ke kusa da jami’ar Oduduwa.

Wani bidiyo ya nuna taliban su na cewa ba su jin tsoron jami’an tsaro, tare da barazanar zaman dirshan a kan tituna har sai an bude jami’o’in.

Daliban sun bayyana takaicin su a kan yadda ake ci-gaba da yajin aikin, sun kuma nuna takaici a kan ‘yan siyasa dangane da yadda su ka kauda kai daga bakatun su, inda ba su taka rawar da ta dace wajen tabbatar da an biya wa malaman jami’o’in bukatun su.

Maimakon haka, sun maida hankali a kan sayen Fom domin tsayawa takara a shekara mai zuwa.

Exit mobile version