Alamu sun nuna bankunan kasuwanci sun shiga jerin masu kin karbar tsofaffin takardun Naira duk da umarnin Kotun Koli.
Kotun Kolin dai ta ba da umarnin tsawaita wa’adin amfani da stoffin takardun Naira na 1,000 da N500 da N200 da aka sauya zuwa ranar Laraba, 15 ga Fabrairu inda za ta dauki mataki biyo bayan karar da aka shigar a gabanta.
Binciken Aminiya ya gano yadda wasu bankunan kasuwacin ke kin karbar tsoffin kudin daga hannun jama’a yayin da suka shiga neman canji a karshen makon da ya gabata a wasu jihohi, ciki har da nan Abuja.
Jihohin Legas da Abuja da Kwara da Ondo da Borno da Imo da Binuwai da Edo da Neja da Ebonyi da Ribas da Oyo na daga cikin jihohin da aka gano bankuna ke kaurace wa karbar tsoffin kudi, lamarin ya shafi har da gidajen mai da manyan kanti kamar yadda bincike Aminiyar ya gano.
A yankin Abuja kuwa, daya daga cikin manajojin bankin ya shaida wa wakilin Aminiya cewa sun rufe wasu sassan bankin su na Zenith ne saboda rashin kudi