Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Sake Fasali: Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Sabbin Takardun Kudi a Yau Laraba

A yau laraba ne shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabbin takardun kuɗi da aka sake wa fasali.

Gwamnan babban bankin Najeriya CBN  Godwin Emefiele      ya ce shugaba Buhari ya ƙaddamar da sabbin takardun kuɗin ne a lokacin taron majalisar zartarwa na ƙasa.

Godwin Emefele, ya ce babban bankin ba zai sauya ranar ƙarshe da ya sa na mayar da tsoffin kuɗin zuwa bankuna domin sauya su da sabbin takardun kuɗin ba.

Tun a ranar 26 ga watan Oktoba ne dai gwamnan babban bankin ya sanar da cewa za a sauya fasalin wasu takardun kuɗi, inda ya ce sabbin kuɗin za su fara yawo daga ranar 15 ga watan Disamba, kuma za a ci gaba da kashe su tare da tsoffin kuɗin har zuwa ranar 31 ga watan Janairun 2023, lokacin da za a daina karbar tsoffin ƙudin.

Exit mobile version