Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

CBN Ya Boye Sabbin Takardun Naira —Gwamnan Jigawa

Gwamnan jihar Jigawa Mohammed Badaru Abubakar, ya zargi Babban Bankin Nijeriya da boye sabbin takardun Naira, lamarin da ya ce ya sa al’ummar jihar ke kwana bin layi domin cirar kudi a na’urar ATM.

Badaru ya bayyana haka ne ta bakin Kwamishinan Kudi da Bunkasa Tattalin Arziki na Jihjar Jigawa Babangida Umar Gantsa, inda ya nuna matukar damuwa da yadda jama’a ke fama da wahalar da bankin CBN ya kirkiro na sake fasalin Naira.

Gwamna Badaru, ya yi zargin bankin CBN ya kwahsi sabbin takardun kudin ya boye, lamarin da ya jefa talakawan sa cikin mawuyacin hali.

Ya ce ‘yan jihar su na fama, saboda harkokin kasuwanci da sauran su sun tsaya sakamakon rashin sabbin takardun Naira, lamarin da ya ce ya kai ga mutane su na kwana a na’urar ATM su na bin layi don neman cire kudi.

Daga binciken da ya yi a bankuna, Gwamnan ya ce ya gano CBN ba ya ba bankunan jihar Jigawa wadatattun sabbin takardun Naira, wadanda ya kamata su loda a na’urar ATM domin amfanin jama’a.

Exit mobile version