Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ci Gaba: Shugaba Buhari Ya Ce a Najeriya Aka Buga Sabbin Takardun Kudi

Shugaba Buhari ya bayyana cewa a Najeriya aka buga sabbin takardun Naira 200, Naira 500 da kuma Naira 500 da ya kaddamar

Shugaban kasa ya ce Kamfanin Buga Muhimman Takardu na Kasa (NSPM) da ya buga takardun kudin ya kara inganta matakan tsaron da ke jikinsu ta yadda buga na jabunsu zai yi matukar wahala.

A jawabinsa a lokacin kaddamar da sabbin takardun kudin, Buhari ya ce wadannan na daga cikin dalilan da suka sa ya amince da bukatar Babban Bankin Najeriya (CBN) na sauya takardun kudin.

Ya kuma jinjina wa Gwamnan CBN, Godwin Emefiele da mataimakansa da suka bukaci tabbatar da sauyin kudaden, da kuma shugabannin kamfanin da ma’aikatansu, “Bisa aikin da suka yi ka’in-da-na’in tare da CBN wajen tabbatar an kammala aikin cikin dan kankanin lokaci.”

A cewarsa, tsarin kudade na duniya ya tanadi a sabunta takardun kudin kasa bayan duk shekara biyar zuwa takwas, amma yanzu kusan shekara 20 ke nan rabon da a yi hakan a Najeriya,Ya kara da cewar Kamar yadda aka sani dokokin babban bankin Najeriya CBN na 2007 sun ta ba wa ba bankin ikon bayarwa da kuma sauya takardun Nair

Exit mobile version