Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Bincike: A Wata 19 Shugaba Tinubu Ya Ciyo Bashin Tiriliyan 50

Tinubu

Tinubu

bincike ya nuna bashin da ake bin gwamantin Najeriya zai ƙaru zuwa Naira tiriliyan 138 a yayin da Shugaban kasa Bola Tinubu ke neman amincewar Majalisar Dokoki ta Ƙasa domin ciyo ƙarin bashin Naira tiriliyan 1.8.

Binciken ya ce cikin wata 19 da Shugaba Bola Tinubu ya yi a kan mulki, gwamnatin sa ta ciyo bashin da ya haura Naira tiriliyan 50, wanda ya zarce rabin wanda ta gada.

A yanzu haka bashin Naira tiriliyan 136 ake bin Najeriya wanda idan majalisa ta amince da buƙatar Tinubu na karɓo bashin Dala biliyan 2.2 daga ƙasashen waje, yawan kuɗin zai ƙaru zuwa tiriliyan 138.

A ranar Talata Shugaba Tinubu ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da takwaran sa na Majalisar Wakilai, Abbas Tajuddeen takardar neman amincewar su da karɓo Karin bashin.

Wasiƙar ta bayyana cewa za a yi amfani da wani ɓangare na kuɗaɗen da za a karɓo ne wajen cike giɓin Naira tiriliyan 9.17 da aka samu wajen aiwatar da kasafin shekarar nan ta 2024.

Wasiƙar ta bayyana cewa karɓo bashin ya dace da tanadin dokar hukumar kula da basuka ta Ƙasa (DMO) ta  2003, kuma ta riga ta samu amincewar majalisar zartaswa ta tarayya.

Exit mobile version