Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Buhari Ya Nemi Amincewar Majalisar Dattawa Ya Biya Bashin Dala Miliyan 556

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya nemi amincewar
Majalisar Dattawa domin ya biya wasu basussukan da ya ce
na tara ne da kotuna daban-daban su ka ci Gwamnatin
Tarayya, amma ba a biya ba.

Buhari ya shaida wa Majalisar Dattawa a rubuce cewa, kotuna daban-daban sun yanke hukuncin a biya kuɗaɗen wasu da naira, wasu kuma da Fam na Ingila, wasu kuma za a biya su da dalar Amurka.

Ya ce kuɗaɗen sun ƙunshi dala dubu 556 da 712 da 584, da Fam na Ingila dubu 98 da 526 da 013, sai kuma naira miliyan 226 da dubu 280 da 801.

Shugaba Buhari dai ya aike da bukatar ne a cikin wata wasiƙa da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya karanta a zaman Majalisar.

A cikin wasiƙar, Shugaba Buhari ya ce kuɗaɗen sun zama bashi ne a wuyan Nijeriya, biyo bayan wasu ƙararraki da aka kai ma’aikatun gwamnatin tarayya da cibiyoyi da hukumomin gwamnati daban-daban a kotuna daban-daban.

Exit mobile version