Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Bangladesh : Shugaba Ya Yi Kiran Da a Kai Zuciya Nesa

OIP (4)

OIP (4)

Shugaban ya yi kira ga samun hadin kan addinai bayan ganawa da mahaifiyar dalibar da ‘yan sanda suka harbe har lahira,

lamarin da ya janyo zanga-zangar da ta kawo karshen mulkin Sheikh Hasina na tsawon shekaru 15.

Yunus mai shekaru 84, da ya taba lashe lashe kyautar Nobel, ya dawo daga Turai a wannan makon don jagorantar gwamnatin wucin gadi,

da ke fuskantar babban kalubale na kawo karshen rikice-rikice da aiwatar da sauye-sauyen demokradiyya.

Hare-haren ramuwar gayya da aka kai kan mabiya addinin Hindu tsiraru a kasar tun bayan hambarar da gwamnatin Hasina,

ya haifar da fargaba a makwabciyar kasar Indiya da kuma fargaba a cikin gida.

A yayin wata ziyara da ya kai birnin Rangpur da ke arewacin kasar, Yunus ya yi kira da a kwantar da hankali,

ta hanyar tunawa da karrama Abu Sayeed, dalibi na farko da aka kashe a rikicin na watan jiya.

Exit mobile version