Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ba Mu Da Masaniyar Ɗaukar Tsohon Ɗan Boko Haram Aikin Tsaron Gidan Kurkuku – Kwanturola

Shugaban Hukumar Kula da Gidajen yari na Ƙasa Halliru Nababa, ya ce ba ya da masaniyar an ɗauki tsohon ɗan kungiyar Boko Haram aikin tsaron gidajen kurkuku.

Tsohon ɗan Boko Haram da ake magana a kai dai shi ne Wilberforce Yohanna, wanda jaridar Premium Times ta buga labarin ɗaukar sa a makon da ya gabata.

Halliru Nababa ya yi iƙirarin na rashin sanin ɗaukar Yohanna ne a lokacin da ake tattaunawa da shi a shafin Tiwitar, bayan mayakan Boko Haram sun kai wa Kurkukun Abuja da ke Kuje hari.

Ya ce ba a sanar da shi cewa Yohanna da ke aiki a Gidan Kurkukun Yola cewa tsohon ɗan Boko Haram ne ba, har sai da ya karanta binciken da jaridar PREMIUM TIMES ta buga.

Sai dai Halliru Nababa ya ce, Hukumar Kula da Gidajen Kurkuku ta Ƙasa ta kafa kwamitin bincike a kan lamarin, ya na mai cewa, gaskiyar magana ba a kai ma shi wani abu mai kama da ɗaukar tsohon ɗan Boko Haram aikin ba.

Exit mobile version