Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

‘Yan Boko Haram Sun Ce Talauci Da Rashin Aiki Ya Haifar Da Ta’Addanci – Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana abin
da wadanda su ka kafa kungiyar Boko Haram su ka gaya ma
shi cewa shi ya haifar da ayyukan ta’addanci tun da farko.

Obasanjo ya ce wadanda su ka kafa Boko Haram a yankin arewa maso gabas, sun shaida ma shi cewa talauci da rashin aikin yi ne ya tursasa su shiga ayyukan ta’addanci.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne, yayin da ya ke jawabi a wajen bikin kaddamar da wani littafi mai suna da ‘yar sa Dakta Kofo Obasanjo-Blackshire ta wallafa a Lagas.

Ya ce a farkon fara Boko Haram, lokacin da aka ce an kashe mutumin da ya fara fafutukar, ya ce ya na so na gana da ‘yan kungiyar domin tattaunawa da su da kuma sanin abin da su ke bukata.

Obasanjo, ya ce ya hadu da wakilan su sannan ya gano cewa ba su bukatar komai face ingantacciyar rayuwa, sai dai ya yi gargadin cewa yawan yaran da ba su zuwa makaranta na iya kasancewa tare da ‘yan Boko Haram a gaba.

Exit mobile version