Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

An Nada Dahiru Ahmed A Matsayin Mai Taimaka Wa Uba Sani A Kan Harkar Yada Labarai

An bayyana nadin da sabon Gwamnan jihar Kaduna Sanata
Uba Sani ya yi wa mataimakain shugaban gidan rediyo da
talabijin na Liberty da ke Kaduna Dahiru Ahmed a matsayin
mafi mahimmanci daga cikin sabbin nade-naden da sabon
gwamnan yi.

Gwamna Uba Sani dai ya nada Dahiru Ahmed ne a matsayin Babban Mai ba shi shawara a kan harkokin gidajen rediyo da talabijin.

Idan dai ba a manta ba, Dahiru Ahmed ya kasance daya daga cikin amintattun ‘yan jaridar da tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ay yi aiki da su a harkokin yada labarai.

Yayin da ya ke karbar sakonnin fatan alheri daga masoya da abokan arziki, Dahiru Ahmed ya bayyana nadin a matsayin hukuncin Allah domin bai nema ba, ya na mai mika godiya da fatan Allah ya fidda shi kunyar gwamnati da daukacin al’ummar jihar Kaduna.

Exit mobile version