An bayyana nadin da sabon Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya yi wa mataimakain shugaban gidan rediyo da talabijin na Liberty da ke Kaduna Dahiru Ahmed a matsayin mafi mahimmanci daga cikin sabbin nade-naden da sabon gwamnan yi.
Gwamna Uba Sani dai ya nada Dahiru Ahmed ne a matsayin Babban Mai ba shi shawara a kan harkokin gidajen rediyo da talabijin.
Idan dai ba a manta ba, Dahiru Ahmed ya kasance daya daga cikin amintattun ‘yan jaridar da tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ay yi aiki da su a harkokin yada labarai. Yayin da ya ke karbar sakonnin fatan alheri daga masoya da abokan arziki, Dahiru Ahmed ya bayyana nadin a matsayin hukuncin Allah domin bai nema ba, ya na mai mika godiya da fatan Allah ya fidda shi kunyar gwamnati da daukacin al’ummar jihar Kaduna.