Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Akpabio Ya Naɗa Wadada Da Adeola Shugabancin Kwamitocin Majalisa

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio, ya sanar da kafa wasu kwamitoci a majalisar domin gudanar da harkokin gwamnati.

Kwamitocin kuwa sun haɗa da na Kasafi da mai kula Asusun Gwamnati da na Ɗa’a da Ƙorafe-ƙorafe.

Da ya ke jawabi yayin zaman majalisar, Akpabio ya bayyana Sanata Solomon Adeola a matsayin Shugaban Kwamitin Kasafi, yayin da Sanata Ahmed Wadada zai jagoranci Kwamitin Kula da Asusun Gwamnati.

Shugaban Majalisar, ya kuma karanto wa zauren wasiƙar da Shugaba Bola Tinubu ya tura wa majalisar ta neman tabbatar da shugabannin tsaron da ya naɗa kwannan nan, inda ya ce majalisar za ta yi aikin tantance shugabannin tsaron daga nan zuwa ranar da bai ambata ba.

Exit mobile version