Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Akpabio Ya Nada Lawan, Kalu, Yari, Tambuwal Da Oshiomhole Shugabancin Kwamitioci

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio, ya
sanar da kafa kwamitin shugabannin riko na majalisar domin
gudanar da wasu ayyuka.

Sanarwar kwamitocin da aka dade ana jira dai ta zo ne, jim kadan bayan tabbatar da nadin ministoci 45 daga cikin 48 da shugaba Bola Tinubu ya mika mata.

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ne zai jagoranci kwamitin tsaro, yayin da Tsohon gwamnan jihar Sokoto Sanata Aminu Tambuwal ke jagorantar kwamitin gidaje, Sanata Adams Oshiomhole kuma zai jagoranci kwamitin harkokin cikin gida.

Sauran sun hada da Sanata Adamu Aliero a matsayin shugaban kwamitin Sufurin kasa, Sanata Gbenga Daniel kuma zai jagoranci kwamitin kula da Sojin Ruwa, sai Sanata Orji Kalu da zai jagoranci kwamitin Ma’aikatu Masu Zaman Kan su, da Sanata Aliyu Ikra Bilbis a matsayin shugaban kwamitin Sadarwa, da Sanata Lawal Usman Mista La da zai jagoranci kwamitin Ilimi.

Exit mobile version