Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Majalisa Ta 10: Tsarin Karba-Karba Na Jam’Iyyar APC Bai Ma Arewa Adalci Ba

Zababben Sanatan mazabar Zamfara ta Yamma kuma dan
takarar Shugaban Majalisar Dattawa Abdul’aziz Yari, ya ce
tsarin karba-karba na jam’iyyar APC a kan mukaman
shugabancin majalisar dattawa ya ci karo da kundin tsarin
mulki na 1999 da aka yi wa kwaskwarima, kuma ya saba wa
ka’idar hukumar daidaito ta tarayya.

Abdul-Aziz Yari, ya ce amfani da addini wajen daidaito a kan rabon mukaman siyasa na jam’iyyar APC kundin tsarin mulkin bai san da shi ba, domin kundin ya ba hukumar daidaito ta tarayya damar kula da daidaito ba manufar addini ba.

Idan dai za a iya tunawa, jam’iyyar APC ta amince da nada Sanata Godswill Akpabio a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa da Mataimakin sa.

Sai dai Abdul-Aziz Yari ya ce tsarin karba-karba na jam’iyyar ya saba wa kundin tsarin mulkin Nijeriya, kuma bai yi wa Arewacin Nijeriya adalci ba, domin duk shugabannin bangarori uku na gwamnati ‘yan Kudu ne.

Exit mobile version