Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta fara gudanar da tsarin tantancewa, tare da bada horo ga wadanda za ta dauka aikin zaben gwamnoni a jihohin Bayelsa da Kogi ranar 16 ga watan Nuwamba.
Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka, yayin wani taron musamman da hukumar ta shirya a kan tsarin daukar ma’aikata da ya gudana a Abuja.
A cewar sa, daukar ma’aikatan wucin-gadi tare da ba su horo ba sabon abu ne ga hukumar ba.
Ya ce zaben ya zo a daidai, kasancewar ba a jima da kammala zaben shekara ta 2019 ba.
Farfesan ya cigaba da cewa, daga cikin hanyoyin da za su iya bi don tabbatar da sahihin zabe, sun hada da tabbatar da ganin an dauki ma’aikatan da su ka dace domin su gudanar da ayyukan zaben.