Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Aƙalla Mutum 20 Sun Mutu A Rikicin Ƙabilanci A Taraba

Rahotanni daga jihar Taraba na cewa, aƙalla mutane ashirin su
ka rasa rayukan su, sakamakon wani rikicin ƙabilanci da ya
ɓarke tsakanin ƙabilun Wurkunawa da Karimjo a ƙaramar
Hukumar Karim Lamido.

A makon da ya gabata ne, gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku ya nada Alhaji Yakubu Abubakar Haruna sanda a matsayin sabon sarki a masarautar Wurkum da ke Karamar Hukumar Karim Lamido.

Shugaban kungiyar ci-gaban al’ummar Wurkum na duniya Wilfred Habuba Yambakam Kwanchi, ya ce dukkan bangarorin da ke rikici da juna sun tafka asara.

Ya ce an dan samu zaman lafiya a cikin gari, amma a kauyukan da Wurkunawa su ke har yanzu ana ta’adi, inda aka kona gidajen mutane sannan an kashe wasu yara.

Wilfred Habuba ya kara da cewa, tuni gwamnati ta tura jami’an tsaro a yankin da lamarin ya faru.

Exit mobile version