Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Kabilanci: Mutane 22 Sun Mutu A Sabon Rikicin Tiv Da Jukun

Akalla mutane 22 aka kashe a wani sabon arangama tsakanin ‘yan kabilar Jukun da Tiv a karamar hukumar Wukari da ke kudancin jihar Taraba.

Tun a makwanni 3 da suka gabata ne al’umomin biyu ke yakar juna, lamarin da ya haddasa hasarar rayuka da dinbin dukiyoyi.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan tawayen Tiv sama da dari biyu ne suka kai musu harin ba-zata, in da suka cinna wa gidaje da dama wuta, suka kuma kashe mutane sama da 10.

Shi ma shugaban karamar hukumar Wukari, Adi Daniel ya tabbatar da harin.

Ko a ranar Litinin da ta gabata, mataimakin gwamnan jihar ya gana da shuagabannin  kabilun biyu domin rattaba hannu kan zaman lafiya, sai dai bayan ganawarsu aka sake kai hari a ranar Talata, baya ga na baya-bayan nan da aka kai.

Exit mobile version