Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ziyara Kasar Qatar: Shugaban Kasa Tinubu Ya Dawo Najeriya.


Jirgin shugaban kasa, ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, da ke Abuja da misalin karfe 7 na yamma. Wannan dai ita ce tafiya ta 12 da shugaban kasa ya yi tun bayan da ya karbi ragamar shugabancin kasar nan a watan Mayun 2023.


Tinubu ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnati da suka hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila; Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.


Sauran sun hadar da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike; Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje da Darakta Janar na Ma’aikatar Harkokin Waje, Yusuf Bichi, da dai sauransu.


A ranar farko ta ziyararsa, Tinubu, ya ziyarci gidan adana kayan tarihi na kasar Qatar, inda ya jaddada muhimmancin adana kayan tarihi.


Tinubu tare da Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, sun rattaba hannu kan wasu yarjejeniya guda bakwai a tsakanin kasashen biyu, bayan ganawar sirri da suka yi a fadar shugaban kasar da ke Doha.

Exit mobile version