Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Zaman Lafiya: Bello Turji Ya Kaddamar Da Hari Kan ‘Yan Bindigar Zamfara

Rahotanni na cewa kasurgumin dan bindiga Bello Turji ya rungumi shirin zaman lafiya na gwamnatin jihar Zamfara a wani yunkuri na kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga a yankin arewa maso yammacin Najeriya.


Mataimakin gwamnan jihar Zamfara Sanata Hassan Nasiha, ne ya bayyana hakan a yayin wani taro kan harkokin tsaro da kungiyar dalibai da wata jami’ar Madina ta shirya a Gusau babban birnin jihar.


Hassan Nasiha ya yabawa Bello Turji bisa matakin da ya dauka na ajiye ayyukan fashi da makami da satar mutane, da kuma matakin taimakawa wajen samar da zaman lafiya a kananan hukumomi uku da ke kan gaba wajen fuskantar hare-hare ‘yan bindiga a jihar Zamfara.


A cewar mataimakin gwamnan, tun makwanni biyar da suka gabata ba a samu wata arangama tsakanin Fulani da Hausawa a kananan hukumomin Birnin Magaji, da Shinkafi da kuma Zurmi na jihar ba, sakamakon tattaunawar sulhun da aka yi tsakanin bangarorin biyu da ke rikici da juna a jihar.


Gidan talibijin na Channels ne dai ya ruwaito mataimakin gwamnan na cewa, kwamitin da Gwamna Bello Matawalle ya jagoranta ya gudanar da taron zaman lafiya da sansanonin ‘yan bindiga tara a gundumar
Magami da Masarautar Dansadau na kananan hukumomin Gusau da Maru a jihar domin su daina kai hare-hare ga mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.


Ya ci gaba da cewa, Turji wanda Gwamna Bello Matawalle ya yi wa afuwa, a yanzu haka yana kaddamar da farmaki kan ‘yan ta’adda a yankunan da suka mamaye domin tabbatar da cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali ya dawo jihar.

Exit mobile version