Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Zaben 2023: Nijeriya Ta Na Bukatar Sauyin Shugabanci – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya sake bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekara ta 2023 karkashin Jam’iyyar PDP.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya sake bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekara ta 2023 karkashin Jam’iyyar PDP.

Yayin da ya ke gabatar da kan sa a wajen wani taro da ya gudana a Abuja, Atiku ya koka a kan abin da ya kira tabarbarewar al’amurra da su ka hada da tsaro da tattalin arziki, wadanda su ka jefa jama’ar kasar nan cikin halin kaka-ni-ka-yi.

Ya ce Nijeriya ta na bukatar sabon jagoranci nagari, wanda zai share wa jama’a hawaye wajen fuskantar matsalolin da su ka addabe su.

Atiku Abubakar, ya ce Allah ya yi wa Nijeriya arzikin da bai dace a ce wani ya yanke kauna dangane da matsalolin da su ka adadbi kasar nan ba, domin kuwa akwai wadanda su ke iya shawo kan su.

Daga cikin wadanda su ka halarci taron akwai tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo, da Gwamnan jihar Adamawa Umaru Fintiri da tsohon Gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu da tsohon ministan harkokin waje Cif Tom Ikimi.

Exit mobile version