Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Zaben 2019: Atiku Ya Lallasa Shugaba Buhari A Jihar Katsina – Majigiri

Shugaban jam’iyyar na jihar Katsina Salisu Maijigri, ya bayyana wa kotun sauraren  kararrakin zaben shugaban kasa cewa Atiku Abubakar ya kada shugaba Muhammadu Buhari a jihar Katsina.

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina Salisu Maijigri

Jam’iyyar PDP dai ta gabatar da Majigiri a matsayin shaidar ta na takwas, wanda ya kasance wakilin jam’iyyar a cibiyar tattara sakamakon zaben shugaban kasa a jihar Katsina.

Yayin da ake yi masa tambayoyi, Maijigiri ya ce sabanin sakamakon da hukumar zabe ta kasa INEC ta sanar, sakamakon da su ka tattara da kan su ya nuna cewa jam’iyyar APC ta samu kuri’u 872,000, yayin da PDP ta samu kuri’u 905,000.

Sakamakon da hukumar zaben ta sanar dai shi ne, cewa jam’iyyar PDP ta samu kuri’ dubu 160 da 203, yayinda APC ta samu kuri’u miliyan 1 da dubu 505 da 633.

Exit mobile version