Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Za Mu Bi Diddigin Yadda Buhari Zai Kashe Bashin IMF – Majalisa

Za Mu Bi Diddigin Yadda Buhari Zai Kashe Bashin IMF - Majalisa

Za Mu Bi Diddigin Yadda Buhari Zai Kashe Bashin IMF - Majalisa

Kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya ce majalisa za ta bi diddigin yadda gwamnatin tarayya za ta kashe bashin da ta karna daga hannun asusun bada lamuni na duniya IMF.

Gbajabiamila ya bayyana haka ne yayin da ya ke ganawa da kungiyoyi masu zaman kansu a ranar Litinin, inda ya ce da haka ne za su tabbata an kashe kudaden bisa tsarin da aka karbo su.

A watan Afrilu ne asusun IMF ya amince da bukatar Nijeriya na neman taimakon kudin gaggawa da suka dala biliyan 3 da miliyan 4 domin cike gibin da ta samu sakamanon barkewar annobar Coronavirus.

Femi Gbajabiamila ya kara da cewa, akwai kudurin dokar farfado da tattalin arziki da majalisar ta ke aiki a kansa a yanzu haka, kuma da zarar ta kammala za ta gabatar da shi domin tattaunawa.

Dokar dai, za ta rage harajin kashi 50 na kamfanonin da ba su sallami ma’aikatan su saboda annobar Corona ba, sannan majalisar za ta dauki duk wani batu da ya shafi yaki da COVID-19 da matukar muhimmanci, wanda yanzu haka kudurin dokar na gaban majalisar dattawa, kuma za a cigaba da tuntuba domin ganin ya zama doka.

Exit mobile version