Rahotanni daga Jihar Kaduna sunce Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce ta ceto ‘yan kasuwa 48 da aka sace a kan hanyar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna a ranar Larabar da ta gabata.
Bayanin Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige ya fitar a ranar Alhamis din nan.
Sanarwar tace an sace ‘yan kasuwar ne sa’ilinda da ayarin motocin ya ke daf da kauyen Udawa.
To sai dai wasu Rahotanni sunce akwai wata mace daya da ba’a san inda ta shiga ba.
Sanarwar ta kara da cewa a Ana ci gaba da kokarin ganin an ceto ta lafiya yayin da kuma za a tura karin ma’aikata zuwa yankin domin kare rayuka da dukiyoyin fararen hula.
Anasa bangaren Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kaduna ya yabawa jami’an bisa jajircewar da suka yi wajen fuskantar hatsari yayin da suke yi wa kasarsu hidima.
Daga karshe ya bukaci su ci gaba da aiki tukuru dakile ayyukan ‘Yan ta’adda a jihar baki daya.

