Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

‘Yan Bindiga Sun Sace ‘Ya’Ya Da Jikokin Sarkin Kagarko A Fadarsa

‘Yan bindiga sun afka fadar Maai Martaba Sarkin Kagarko da
ke jihar Kaduna Alhaji Sa’ad Abubakar, inda su ka yi awon
gaba da ‘ya’yan sa 9, wadanda su ka hada da jikokin shi da
wasu mutane na daban.

Rahotanni sun ce, ‘yan bindigar sun sace amaryar sarkin, wadda daga bisani ta kubuta daga hannun su tare da komawa gida kamar yadda wadanda su ka shaida lamarin su ka bayyana.

Rahotanni sun ce ‘yan ta’addan sun kuma kashe wani makiyayi a kauyen Kuchimi, sannan su ka sace kayayyaki na akalla shaguna bakwai a kauyen Janjala da ke Karamar Hukumar Kagarko.

Jihar Kaduna dai ta na daya daga cikin joihohin arewacin Nijeriya da su ka fi fama da hare-haren ‘yan bindiga.

Exit mobile version