Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

‘Yan Bindiga Sun Kashe Matar Aure, Sun Sace Mutum 6 A Abuja

Wasu masu garkuwa dsa mutane sun shiga gidaje inda suka kashe wata matar aure tare da sa sace wasu mutum shida a yankin Kwali da ke Abuja.

Wani mazaunin yankin mai suna Yakubu Saidu, ya ce ’yan bindigar sun fara ne da shiga wasu gidaje biyu suka sace mutum biyu tare bude wuta cikin daren ranar Talatar da ta gabata.

Ya kara da cewa Daga nan suka shiga gidan wani dillalin motoci, Amma ba su same shi ba saboda ya tsere, inda suka yi awon gaba da kannensa maza biyu.

A cewarsa, a ranar Laraba kuma ’yan bindiga sun sake zuwa yankin da misalin karfe 11:23 na dare inda suka kashe matar a lokacin da take kokarin tserewa.

Wasu daga cikinsu maharan sun shiga wasu gidajen suka yi garkuwa da mutum uku.

Duk kokarin da aka yin a jin ta bakin kakakin ’yan sandan Abuja, DSP Adeh Josephine, yaci tura.

Exit mobile version